✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hori ’yan kwallon Nasarawa United su kara kwazo

An yi kira ga ’yan kwallon Nasarawa United da masu horar da su da su yi kokarin ganin sun saka wa gwamnatin Jihar Nasarwa ta…

Alhaji Muhammadu Alkali Shugaban Kungiyar Nasarawa UnitedAn yi kira ga ’yan kwallon Nasarawa United da masu horar da su da su yi kokarin ganin sun saka wa gwamnatin Jihar Nasarwa ta hanyar zage damtse a wasannin da suke yi don ganin  kwalliya ta biya kudin sabulu.
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United Alhaji Muhammadu Alkali ne ya bayyana haka a lokacin da suka tattaunawa da wakilinmu a kan harkokin wasanni a jihar.
Alhaji Muhammadu ya kara da cewa, wannan kira ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yadda gwmanatin Jihar take kashe makudan kudi a kan kulob din Nasarawa United musamman a kan ‘’yan wasan da kuma masu horar da su.
Ya ce a kwanan nan ne Gwamna Umaru Tanko Al-makura ya biya kashi 50 daga cikin 100 na kudin ’yan wasa da masu horar da su watau signing fees.  Shugaban ya ce, yana da tabbacin gwamnan ne kadai daga cikin gwamnonin kasar nan da ya biya ’yan wasan rabin hakkokinsa kawo yanzu.
Sannan Gwamna Al-makura ya sayo wa kulob din sabuwar mota mai kwasar mutum 26 ga kulob din na Nasarawa United.  Sannan Gwamna ya kara yawan kudin alawus-alawus na ’yan kwallon watau ‘match bonus’ da kuma na cin abinci.
Shugaban ya ce, gwamnan yakan biya ’yan wasa alawus da sun samu nasara a duk wasan da suka yi ba tare da bata lokaci ba (winning match bonus).  
Wadannan dalilai ne suka sa shugaban yin kira ga ’yan wasan da jami’ansu da su tabbatar kwalliya ta biya kudin sabulu ta hanyar sakawa gwamnan wajen yin abin a-zo-a-gani a wasannin da suke yi.
Da yake tsokaci a bisa koma bayan da kulob din ya samu a gasar rukuni-rukuni ta kasa kuwa, Shugaba Alhaji Muhammadu Alkali ya ce, kulob din yana fuskantar matsala ne tun bayan da ya samu koma baya a kimanin shekaru uku da suka gabata inda zuwan Gwamna Tanko Al-makura ne ya fa kulob din ya fara farfadowa a halin yanzu, don haka akwai bukatar a samu lokaci kafi kulob din ya gama farfadowa.  “Saboda kaunar da Gwamnan yake da shi ga harkar wasan kwallon kafa ce ta sa yake kula da kulob din a wannan lokaci kuma nan gaba kadan za a ga canji”, inji shi.
Daga nan sai shugaban ya yi kira ga magoya bayan kulob din da su cigaba da ba shi da had in kai da goyon baya don ganin sun samu nasara a dukkan wasannin da suke yi a ciki da wajen jihar.