✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An jaddada muhimmancin koyar da ilimi ta amfanin da harshen uwa

Shugaban Hukumar Bunkasa Ilmin Firamare ta kasa reshen Jihar Zamfara, Alhaji Murtala Adamu Jangebe ya nemi a kara himma wajen fito da dubarun koyarwa, mussaman…

Shugaban Hukumar Bunkasa Ilmin Firamare ta kasa reshen Jihar Zamfara, Alhaji Murtala Adamu Jangebe ya nemi a kara himma wajen fito da dubarun koyarwa, mussaman amfani da harshen uwa don koyar da yara kanana sanin abin da suke koyo daga aji daya zuwa uku.

Shugaban ya fadi haka ne a yayin kammala gasar nuna hazaka da koyon karatu da harshen uwa ga yara yan aji 1-3 na makarantun firamare da masu yaki da jahilci da aka gudanar a Gusau, Jihar Zamfara a ranar Talatar da ta gabata.

A sakonsa na fatan alheri ga taron gasar, Babban Sakataren Hukumar Ilmi na kasa Dokta Hameed Bobboyi, wanda Babban Jami’insa Alhaji Abdullahi Jibo Birnin Yawuri ya wakilta, ya yabo ga Hukumar Ilmin Firamare ta Jihar Zamfara dangane da kokarin da ta yi na bai wa masana dama ta amfani da shirin bunkasa karatu da karin masu koyo. Ya ce Hukumar UBEC za ta ci gaba da bayar da hadin gkiwa tare da talalfawa ga dukkanin masu neman hada hannu don ciyar da ilmin firamare gaba.

A jawabinsa na fatan alheri, Sarkin Fulanin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru ya nuna kudurinsu na sarakunan gargajiyya ga tabbatar da samun nasara ga wannan shirin tare da jijjina ga hukumomin bayar da tallafi dangane da bunkasa ilmin yara kananan don samun shugabannin da suka dace a gobe.

Tun da farko a jawabinsa ga mahalarta gasar, babban jami’i mai kula da shirin na karatu da samar da hanyoyin bunkasa ayyukan ilmin yara da ake wa take da ‘RANA’ Dokta Mika’ilu Ibrahim ya nuna godiyarsa dangane da hadin kai da fahimtar da aka samu tsakanin Hukumar Bunkasa Ilmin Firamare ta Jihar Zamfara da cibiyoyin bayar da tallafi na UKaid, UNICEF da FHI360, wadanda suka samar da nasara a wajen tabbatar da gasar.

Ya ce shirin RANA na ilmantar da yara tare da amfani da wasu dubaru na koyarwa da harshen uwa na Hausa, yana da asali ga shirin bunkasa ilmi a cikin al’umma, a wasu jihohin Arewa.

A jawabinta uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Asmau Abdul’azeez Yari ta hannun Farfesa Balkisu Aminu ta yaba ma kungiyoyin bayar da agaji na kasashen waje dangane da sha’awar da suka nuna don ciyar da ilmin yara kanana ba a jihar.

dalibai ’yan kimanin shekara 10 zuwa 12 tare da wasu dattawa ne suka fafata wajen nuna hazaka a karatun hikayoyin Hausa daga littattafan Magana Jari Ce da Iliya dan Mai karfi da sauransu a gasar, inda Muhammadu Aliyu dan shekara 12 daga Gusau ne ya lashe gasar karatun hikaya na Hausa, yayin da Malama Balkisu dahiru daga ajin Yaki Da Jahilci ta lashe kyauta ta daya a matakin manya.

An gabatar da wake-wake na Hausa da kuma sakonnin fatan alheri daga sarakunan gargajiyya da kuma manyan masu rike da mukaman gwamnati na jiha da tarayya.