✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An jefa matashi gidan yari saboda rungumar Cristiano Ronaldo

Wani matashi mai suna Ronald Gjoka, mai kimanin shekara 19 ya samu matsala bayan ya keta cikin filin kwallo a lokacin da ake gudanar da…

 Cristiano RonaldoWani matashi mai suna Ronald Gjoka, mai kimanin shekara 19 ya samu matsala bayan ya keta cikin filin kwallo a lokacin da ake gudanar da kwallo a tsakanin kulob din Real Madrid da ke Sifen da na Chelsea da ke Ingila a karshen makon jiya kuma ya rungume shahararren dan kwallon Madrid Cristiano Ronaldo.
Al’amarin ya faru ne a daidai minti 67 a lokacin da kungiyoyin biyu suke fafatawa  a wasan karshe na sada zumunta a Amurka a gasar da ake wa lakabi da International Champions Cup a lokacin da matashin ya yi wuf ya fada cikin fili kuma bai tsaya a ko’ina ba sai wajen Ronaldo inda ya rungume shi don soyayyarsa ga dan kwallon.
Sai dai jami’an tsaro sun yi ram da shi inda ba su yi wata-wata ba suka aika da shi gidan yari saboda laifin shiga filin wasa ba tare da izini ba da kuma tayar da hankalin al’umma.
Rahoton da kafar sadarwar Naij.com ta kalato ya nuna matashin ya  shafe daren ne a tsare sai dai an sake shi da safe.
Sai dai matashin ya nanata cewa zai jajirce duk irin barazanar da za ta same shi muddin a kan Cristiano Ronaldo ne. Ya ce idan ya samu dama zai maimaita abin da ya yi ba tare da yin nadama ba.
“A gaskiya, tun farko na dade ina tunanin yadda zan hadu da dan kwallon gaba-da-gaba don haka da na samu dama sai na yanke shawarar aukawa filin wasa, kuma yanzu na biya bukata ta”.
“Lokacin da na rungume shi na roke shi kada ya bar jami’an tsaro su kama ni amma kafin ka ce kwabo sun yi ram da ni, amma duk da haka na fada masa cewa na yi matukar murna da na samu damar rungume shi a rayuwata kuma Ronaldo ya yi murna da jin kalamai na”.
Ronaldo ne ya jefa kwallaye biyu daga cikin ukun da kulob din Madrid ya doke na Chelsea a wasan karshen. An tashi wasa ne da ci 3-1.