✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da cibiyar sasanta rigingimun jama’a a Katsina

An kaddamar da Cibiyar Sasanta Rigingimun a Tsakanin Jama’a,  “Community Conflict and Dispute Resolution Centre- CCDRC)” a Jihar Katsina. Babban Jojin Jihar Mai shari’a Musa…

An kaddamar da Cibiyar Sasanta Rigingimun a Tsakanin Jama’a,  “Community Conflict and Dispute Resolution Centre- CCDRC)” a Jihar Katsina.

Babban Jojin Jihar Mai shari’a Musa Danladi Abubakar ne ya kirkiro tare da kafa wannan cibiya domin rage yawan rigingimun da suke faruwa a tsakanin jama’a. Cibiyar za ta kasance ne a karkashin kular Kotun Sasanci (Katsina Multi Door Courthouse) inda za a rika bayar da dama ga al’ummar jihar su gabatar da koke-kokensu kan al’amuran zamantakewa domin su sasanta.

Da yake yi wa wakilin Aminiya karin haske kan abubuwan da cibiyar za ta aiwatar, Babban Jojin ya ce akwai ka’idodin da aka gindaya za a yi amfani da su wajen tafiyar da cibiyar da take ta gwaji ce da aka yi a tsakanin rukunin al’ummar Kabakawa da Kwado da Makera, dukkansu da ke cikin garin Katsina. Ire-iren rigingimun da cibiyar za ta rika yin sasancin a kansu ba tare da an kai ruwa-rana ba, sun shafi makwabtaka. “Har ila yau, cibiyar za ta sasanta rigingimun aure da bashi da fadan yara da rigima tsakanin ’yan uwa da sauransu. Cibiyar za ta saurari rigingimun da ’yan sanda da masu gari da malaman makaranta da jami’an gwamnati tare da kungiyoyin matasa domin shiga tsakani,” inji shi

Ya ce ban da sasanta kananan rigingimu, cibiyar za ta gudanar da wasu ayyuka na musamman da suka hada da tantacewa da kuma amincewa ga duk wanda zai bayar da gidan haya ko kuma sayarwa, ta hanyar tabbatar da halayyarsa, wurin aiki ko sana’a da sauran irinsu domin samun nagari ba wanda zai cutar da al’umma ba. “Sannan yana da kyau jama’a su sani cewa duk ayyukan da cibiyar za ta yi kyauta ne ga al’umma. Saboda haka, kofar cibiya a bude take,” inji shi.