✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da makarantar ‘almajiri model primary’ a Benin

A tsakiyar makon jiya ne darakta a ma’aikatar Ilimi mai kula da ilimin firamare a Jihar Edo, Misis J. E. Ogiedegbe ta kaddamar da malamai…

Wasu daga cikin daliban sabuwar makarantar ta ‘Almajiri model primary’ a cikin ajiA tsakiyar makon jiya ne darakta a ma’aikatar Ilimi mai kula da ilimin firamare a Jihar Edo, Misis J. E. Ogiedegbe ta kaddamar da malamai masu koyarwa a sabuwar makarantar da gwamnatin tarayya ta gina mai ajujuwa shida ta ‘Almajiri model primary’ a Zangon Eyaen a birnin Benin.
Sabuwar makarantar an bude ta tare da dalibai kimanin metan, maza da mata, kuma tana da malamai masu koyar da ilmin zamani biyar har da shugabar makarantar, Madam Paulina O. Dika; sai masu koyar da harshen Larabci da na addinin Musulunci.
A wajen taron kaddamarwar manyan ma’aikata na hukumar ilimin firamare na jihar da na karamar Hukumar Uhonmwode suka rufa wa daraktar baya zuwa bude makarantar, inda aka yi jawabai masu gamsarwa da kira kan batun tura yara zuwa makaranta da nuni kan amfanin ilimi ga rayuwar dan Adam.
Misis Ogiedegbe,n a cikin jawabita, ta nemi iyaye da sauran jama’a su baiwa shirin gwamnati na ciyar da ilimi gaba goyon baya da hadin kai, musamman wajen jajircewa kan tura yaransu zuwa makaranta koyaushe. Sannan ta nemi malaman da su tsaya tsakani da Allah su koya wa yara ilimi mai nagarta tare da ba su tarbiyya ta kwarai da cusa musu akida ta kirki.
Sai ta ce ya wajaba malaman da iyayen yara su hada kai domin ta haka ne kurum yaran za su samu su tsira da ilimi mai inganci da zai amfane su kuma ya amfani kasa baki daya.
A karshe ta gode wa shugabannin al’ummar ’yan Arewa da suka halarci bude makarantar  da iyayen yara da sauran jama’a baki daya.