✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da sabuwar jaridar Muryar ’Yanci

Shugaban kamfanin sadarwa da ake kira da turanci ATAR Communications Nigeria Limited da ke yada shirye-shirye a gidajen rediyo da talabijin na Liberty, Dokta Ahmed…

Shugaban kamfanin sadarwa da ake kira da turanci ATAR Communications Nigeria Limited da ke yada shirye-shirye a gidajen rediyo da talabijin na Liberty, Dokta Ahmed Tijjani Ramalan ya kaddamar da sabuwar jaridar Hausa mai suna Muryan ’Yanci da ta turanci mai lakabin boice of Liberty.

Da yake kaddamar da sabuwar jaridar a ofishinsa da ke Abuja, Dokta Ramalan ya bayyana cewa sun bullo da sababbin jaridun ne don tsage gaskiya komai dacinta. “Sabuwar jaridarmu ta Hausa ta Muryar ’Yanci da ta turanci bioce of Liberty Newspaper kafofi ne da za su rika tsage gaskiya komai dacinta tare da baiwa kowane bangare hakkinsa don wallafa labaran gaskiya ba tare da tsoro ko goyon bayan wani bangare ba”. In ji shi.

Ya kara da cewa “Za mu tabbatar da cewa jaridun sun baiwa kowa hakkinsa tare da bayar da damar fadin albacin baki da kuma ’yancin fadar ra’ayi kamar yadda kundin tsarin dokokin Najeriya ya tanadar don bunkasar kasa baki daya”.

Haka kuma ya bayyana cewa sun dauki matakan da suka kamata don tabbatar da cewa jaridun sun samu karbuwa a wurin jama’a da kuma kamfanonin tallace-tallace.

Ya ce kasancewarsa wanda ya kafa gidan rediyo da talabijin wanda ya samu karbuwa a wurin jama’a zai yi amfani da kwarewarsa don ganin cewa jaridun sun dore tare da samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya da bunkasar tattalin arzikin kasa.

 Da yake jawabi, daya daga cikin manyan baki, Peter Igho ya yaba wa Dokta Ramalan kan namijin kokarin da yake yi na bunkasa harkar yada labarai tare da samar da ayyukan yi ga jama’a.

Wadanda suka yi bayani a wurin taron sun taya Dokta Ramalan murna kan yadda yake samun ci gaba a harkokin yada labarai tare da tallafa wa jama’a. Sun yi fatan jaridun biyu za su dore tare da tsayawa kan gaskiya ba tare da nuna bangaranci ba.

Jaridar Muryar ‘Yanci na wallafa labaranta ta kafar yanar gizo ita kuwa ta turancin mai suna bioce of Liberty na fitowa mako-mako kuma ana sayar da ita a ko’ina a fadin kasar nan tare da wallafa labaranta ta kafar yanar gizo.