Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An kafa sabuwar gwamnati a Mali

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita

Rahotanni daga kasar Mali  sun ce Firayi Ministan kasar Boubou Cisse ya kafa sabuwar gwamnati kamar yadda Shugaban Kasar ya dora masa nauyi.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Mali Mustafa Ben Barka ya fitar ta tashar talabijin din kasar ta ce akwai ’yan Majalisar Zartarwa 38 da suka hada da Firayi Minista Cisse a cikin sabuwar gwamnatin.

ADVERTISEMENT

Ben Barka ya kara da cewa akwai mata da ’yan adawa sama da 10 a cikin sababbin ministocin da aka nada.

A sabuwar Majalisar Ministocin, Firayi Minista Cisse ne zai rike Ma’aikatar Ci gaban Tattalin Arziki da Kudi sai Michel Hamala Sidibe, Ministan Lafiya da Al’amuran Zamantakewa da  Malick Coulibaly na Shari’a da Kare Hakkokin dan Adam, da Manjo Janar Ibrahim Dahirou Dembele na Tsaro da Harkokin Soji sai Tiebile Drame da aka nada Ministan Harkokin Kasashen Waje da Alakar Kasa da Kasa da Hadin Kai, kamar yadda kafar labarai TRT ta ruwaito.

ADVERTISEMENT

Bayan tsohon Firayi Ministan Mali Soumeylou Boubeye Maiga ya yi murabus a ranar 18 ga Afrilu ne Shugaban Kasar Ibrahim Boubacar Keita ya ba wa Cisse aikin kafa sabuwar gwamnatin.