✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai hari ofishin ‘yan sanda an kashe DPO da wasu mutum 3 a Bayelsa

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a safiyar yau Litinin sun kai hari ofishin ‘yan sandan unguwar Agudama- Ekpetiama da ke Karamar Hukumar Yenagoa…

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a safiyar yau Litinin sun kai hari ofishin ‘yan sandan unguwar Agudama- Ekpetiama da ke Karamar Hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa inda suka kashe jami’an ‘yan sanda hudu dake bakin aiki.

Cikin wadanda aka kashe a harin, akwai jami’in ‘yan sandan yankin DPO da wata jami’ar ‘yar sanda mai juna biyu da kuma wasu jami’an ‘yan sanda biyu dake bakin aiki a lokacin.

Wani daga yankin da yaso a sakaya sunansa ya bayyanawa majiyar mu cewa, babu wani farar hula da aka raunata yayin kai harin, an kai harin ne da misalin karfe 2:15 na tsakar daren yau.

Kakakin Hukumar ‘yan sandan jihar SP Asinim Butswat, ya tabbatar da aukuwar harin kuma ya ce, a yanzu haka ana gudanar da bincike.