✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai karar Majalisar Dokoki kan sayen motocin alfarma

Kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa da na kare hakkin dan Adam da kuma wadansu ’yan kishin kasa su 6,721 sun shigar da kara…

Kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa da na kare hakkin dan Adam da kuma wadansu ’yan kishin kasa su 6,721 sun shigar da kara a gaban kotu a kan yadda ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa za su kashe Naira biliyan biyar da rabi wajen sayen motocin alfarma.

Kungiyoyin sun shigar da karar ce suna so a haramta wa majalisar kashe wadannan makudan kudi, saboda hakan ya saba wa sashi na 57 (4) na tsarin sayayyar kayan amfani na shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa da ke kundin tsarin mulkin majalisar na shekara 2007.

Kungiyoyin sun ce ya zama wajibi majalisar ta zabge yawan kudin da take so  ta sayi motocin da su.

Daya cikin ’ya’yan kungiyoyin, Salihu Dantata Mahmood, ya ce ba zai yiwu suna ganin talauci da yunwa da rashin biyan kudaden makarantan yara da rashin magunguna suna daidaita mutane sannan su yi shiru ba, domin an zabe su ne su yi dokokin da za su canja rayuwar al’umma ba kashe kudi barkatai ba.

Kwamared Bako Abdul, wanda ya ke wakiltar Kungiyar Campaign for Democracy (CD), a lokacin shigar da karar ya ce almubazaranci ne, barin ’yan majalisar su sayi motocin. Ya kara da cewa, ’yan majalisar su yi maza su janye wannan kudiri na sayen motocin domin su wakilan jama’a ne ba wakilan kansu ba.