✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai karar surukin Lionel Messi

Wata mata da ba a tantance sunanta ba ta kai karar surukin Lionel Messi, Jose Roccuzzo a gaban wata kotu a Ajantina inda take naman…

Wata mata da ba a tantance sunanta ba ta kai karar surukin Lionel Messi, Jose Roccuzzo a gaban wata kotu a Ajantina inda take naman ya biya ta Fam dubu 40 kwatankwacin Naira miliyan 18.

Jose Roccuzzo shi ne mahaifin matar Lionel Messi mai suna Antonella.

Matar wadda take aiki a katafaren shagon surukin Messi inda ta kwashe sama da shekara 20 an wayi gari ya sallame ta ce ba tare da ya biya ta hakkokinta ba.

Katafaren shagon wanda yake a Rosario da ke Ajantina inda aka haifi Lionel Messi da matarsa Antonella, yana da ma’aikata masu yawa da ke aiki a karkashinsa, kuma matar tana daya daga ciki.

Rahotanni sun ce matar ta fara samun matsala da surukin Messi ne bayan ta yi hadarin mota a bara, wanda hakan ya sa ba ta iya zuwa wajen aiki a kan lokaci.

Kamar yadda lauyanta Bernando Lerroud ya shaida wa manema labarai ya ce, yana kare matar ce ganin yadda aka zalunce ta bayan ta shafe fiye da shekara 20 tana aiki a katafaren shagon ba tare da an sallame ta ba.

“Duk kokarin da ta yi wajen ganin an biya ta hakkokinta abin ya ci tura, dalili ke nan ta gabatar da batun a gaban alkali,” inji lauyan.