✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai Sanata Yarima kotu bisa zargin fashi da makami

An gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura a gaban kotu ana zarginsa da aikata manyan laifuffuka ciki har da fashi…

An gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura a gaban kotu ana zarginsa da aikata manyan laifuffuka ciki har da fashi da makami.
karar wadda aka ajiye ranar 13 ga Janairu mai zuwa domin ci gaba da sauraronta ana tuhumar Sanata Yarima da wasu mutum 29 bayan da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya shigar da kararsu a ranar Juma’ar da ta gabata  a Babbar Kotun Jiha da ke Gusau inda Mai shari’a Kulu Aliyu ke shugabanci.
Kafin Mai shari’a Kulu Aliyu ta dage shari’ar, mai gabatar da kara Oluye Torugeber Samuel, ya shaida wa kuton cewa “Sufeto Janar na ’Yan sandan yana karar Sanata Yarima da wasu mutum 29 bisa tuhumarsu da aikaa babban laifi.”
Mai shari’a Kulu ta amshi takardar karar kuma ta umarci mai gabatar da karar ya kawo cikakkun bayanai ga wadanda ake kara daya bayan daya zuwa 13/01/2014, da za a ci gaba da sauraron shari’ar.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Lauyan tsohon Gwamnan, Barista Sani Kato ya ce ana karar tsohon Gwamnan da mutum 29 da aikata manyan laifuffuka da kuma fashi da makami.
Da yake tofa albarkacin bakinsa jin kadan da gabatar da karar Sanata Ahmad SaniYariman Bakura ya ce “Wannan jarrabawa ce da mutum ke samu kuma haka rayuwa take, sai an jarrabe ka, kuma dama an ce ka guji sharrin wanda ka taimaka masa.”
Ya ce, dan majalisar tarayyya “Ibrahim Shehu ya kai ni kara cewa ni na sa aka yi masa wulakanci, ya rage ga kotu ta gani idan akwai inda na sa a yi wa wani wulakanci ba ma shi kadai ba.”