✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir gidan yari

An kai tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir gidan yarin Kobar mai cike da tsaro, kwanaki kadan bayan da sojoji suka hambarar da shi daga mulki.…

An kai tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir gidan yarin Kobar mai cike da tsaro, kwanaki kadan bayan da sojoji suka hambarar da shi daga mulki.

Rahotanni sun ce kafin wannan lokacin dai an tsare shugaban ne bisa daurin talala a Fadar Shugaban Kasar. An ruwaito cewa an tsare shi karkashin sa idon jami’an tsaro.

Watannin da aka shafe ana zanga-zanga a Sudan ya jawo aka hambarar da shugaban tare da tsare shi.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Uganda Henry Oryem Okello, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa kasarsa za ta duba yiwuwar bai wa al-Bashir mafakar siyasa, duk da sammacin da Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC) ta aike masa.

Sai dai a matsayinta na mamba a ICC, dole ne Uganda ta mika Mista Bashir ga kotun idan har ya shiga kasar. Har yanzu dai ICC ba ta ce komai ba kan batun.

Kafin yanzu, ba a san inda Bashir yake ba. Jagoran juyin mulkin Awad Ibn Auf, ya ce ana tsare da shi ne a wani “amintaccen waje,” kamar yadda BBC ya ruwaito.

Sai dai shi ma daga baya ya sauka daga mukamin nasa.

Daga bisani sai aka nada Laftana Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya, inda ya zama shugaban Sudan na uku cikin kwan biyu.

Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin ci gaba da mamaye titunan kasar har sai an samu sauyin mulki zuwa na farar hula.