✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ango da amarya kan ba da mafaka ga masu garkuwa da mutane

Al’ummar Unguwar Jiwafa da ke Sabon Garin Marabar Gurku a Jihar Nassarawa na ci gaba da zaman dar-dar, mako biyu bayan samamen ’yan sanda a…

Al’ummar Unguwar Jiwafa da ke Sabon Garin Marabar Gurku a Jihar Nassarawa na ci gaba da zaman dar-dar, mako biyu bayan samamen ’yan sanda a unguwar inda suka yi awon gaba da wani ango da amaryarsa da wadansu bakin mata uku da ake zargin sun ba su mafaka.

Lokacin da Aminiya ta ziyarci unguwar a ranar Talatar da ta gabata, yawancin mazauna wajen sun ki amincewa su yi bayani kan lamarin gudun abin da ka je ya zo.

Sai dai wakilinmu ya samu nasarar gano gidan ma’auratan, sai kuma wani gidan kasaita da aka kama bakin matan tare da maigadin gidan.

Malama Ummu Salma ita ce uwargidan Adamu soja wanda ta bayyana shi a matsayin direban sojoji da ke aiki a Barikin Mogadishu da aka fi sani da Barikin Abacha a Abuja, ta ce mijinta ya auri amaryar ce mako uku da suka gabata. “Da ma mahaifinta bai jima da zuwa unguwar nan ba, sai ya sanar da maigidana cewa yana so zai aurar masa da ’yarsa bayan yaba halinsa. To sai maigidana ya nemi shawarata, ban nuna damuwa a kai ba bayan ya ce ya gamsu da tarbiyyar gidan. To a ranar da lamarin zai faru sai surukinsa wato baban amarya ya bukaci ya bai wa bakinsa wajen kwana kafin su wuce. To wannan shi ne dalilin da mijina ya shiga makwabta, ya nemi waje ya saukar da su. Daga baya ne nake samun labarin cewa an kashe tsohon mijin amaryar ne a wani artabu da jami’an tsaro da masu garkuwa da mutane, sannan shi kansa uban amaryar, jami’an tsaro suna nemansa.

“Mijina direban sojoji ne kuma yana da matsayin saje. ’yan sandan sun shigo gidan nan kamar karfe 2:00 na dare kuma tun a nan suka yi masa duka da lahanta shi a hannu. Sun dauki takardarsa ta shaidar aiki da hotuna da sauran kayan aikinsa, sai kudina na sana’ar da nake yi kamar Naira dubu 10, ba inda ba su bincika ba a dakunanmu, kuma ba wani mummunan abu da suka samu,” inji ta.

Ta ce, “Tunda aka kama shi yau kwana 13 ke nan ban ji labarinsa ba, yanzu haka ba mu da komai ga ’ya’yanmu biyar duk sun galabaita sakamakon fargabar tafiya da mahaifinsu da aka yi.”

Aminiya ta ziyarci gidan da aka saukar da bakin matan inda Malama Hauwa’u Sulaiman Madaki ta bayyana yadda aka kawo su da kuma kama su. “Mijina Malam Yahaya mai gadi ne a wannan gida, kuma mu kadai ne a ciki. Ba mu san ainihin mai gidan ba saboda wani ne ya yi wa maigidana hanyar aiki a wajen. To a ranar Talatar, yau mako biyu ke nan sai Adamu Soja ya zo gidan nan da yamma ya yi sallama yana tambayar maigdana. Na ce da shi ba ya nan. Bayan Sallar Magariba sai ya sake dawowa, amma bai same shi ba, ya tambayi lambar wayarsa, na ce wayata ta lalace kuma ban rike lambarsa a kai ba. To a nan ne ya ce mu yi hakuri ya yi bakin ba-zata ne, za su zauna a wajenmu na kwana daya kafin ya sama musu waje, to ni dai ban ce da shi komai ba,” inji ta.

Ta ce, “Bayan Sallar Isha’i sai matansa suka kawo bakin mata su uku, na nuna musu wani daki suka yi shimfida suka kwanta. Maigidana bai dawo ba har lokacin da na yi barci. Sai da misalin karfe 3:00 na dare da na farka sai na sanar da shi cewa dazu Adamu Soja ya zo yana tambayarka da kuma neman alfarma kan zai kawo wadansu baki, sai dai kafin  in karasa bayanin ba sai ga kanwarsa ta shigo inda muke, ta sanar da mu cewa wadansu sun shigo cikin gidan. Ban sani ba ya kai ga fahimtata ko bai fahimce ni ba, sai kawai ya tashi a firgice, yana fita sai suka ce ina baki? Sai ya ce musu ba baki, saboda shi bai sani ba, sai suka banke shi suka shige cikin dakuna. Sun yi ta yaye labulen dakuna sai ga matan sun tattara kansu da ’ya’yansu a wani ban-daki da  ba a fara amfani da shi ba. To a nan suka fito da su waje, sannan suka fuskanci maigida suka ce karya za ka yi mana. Sun kuma tambaye shi Baban Nura, ya ce da su shi bai san Baban Nura ba. To sai suka ce za su wuce da shi tare da matan kuma ba za su sako su ba sai Baban Nura ya kai kansa.”

Kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, Frank Mba kan lamarin bai samu nasara ba, saboda bai dauki waya ba ko amsa sakon da wakilinmu ya aika masa har zuwa lokacin hada wannan rahoto.