Da Dumi Dumi

An kama barayin takin zamani

Rundunar ‘yan sandan Legas ta kame wasu mutum uku da ake zargi da satar takin zamani buhu 300 wanda suka yi yunkurin yi suka sayarwa wasu ‘yan kasuwa a jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Legas DSP Bala Elkana, ya shaidawa Aminiya cewa rundunar ta kame mutunen uku ne a ranar 24 ga watan jiya biyo bayan wani koke da mai lura da runbum masana’antar fulawa ta Iganmu ya shigar wa ofishin rundunar da ke Bode Thomasa yankin Surulere, inda ya shaida cewa an fasa runbum an sace takin zamani buhu 300, “Nan da nan jami’anmu su ka isa masana’artar bayan binciken da suka yi sun gano cewa, akwai hadin bakin wasu da ke aiki a wajan inda binciken ya gano an kwashi takin a jimbge a wani runbum ajiya a kasuwar Daleko da ke Munshin inda aka sayarwa wasu ‘yan kasuwa daga Kano akan kowa ne buhu Naira dubu 4, jami’an mu sun isa wajen ne a daidai lokacin da ake oda babbar motar da zata kwashe takin inda suka yi awon gaba da ita tare da wadanda ake zargi da hannu a badakalar.” In ji shi.

Ya ce, wadanda ake zargin sun hadar da: Prince Banjo Adeleke mai shekaru 57 dan asalin yankin Ijebu a jihar Ogun sai James Daled mai shekaru 52 mutumin Mangu a jihar Filato da Haladu Junaidu mai shekaru  52 dan asalin kararamar hukumar Dala a jihar  Kano, ya ce ana ci gaba da bincikar lamarin kafin daga bisani a gurfanar da su a kotu.

Share