✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan fasakwabrin da ya kashe jami’in Kwastam a Ogun

Hukumar Kwastam ta yi nasarar kame daya daga cikin ‘yan fasakwabrin da ake zargi da harbe jami’inta mai suna Yakubu Shu’aibu a jihar Ogun Jami’an…

Hukumar Kwastam ta yi nasarar kame daya daga cikin ‘yan fasakwabrin da ake zargi da harbe jami’inta mai suna Yakubu Shu’aibu a jihar Ogun Jami’an rundunar na jahar Ogun ne suka yi nasarar kame wanda ake zargin da kashe jami’in rundunar tare da jikkata wani a karshen makon jiya.

Mai magana da yawun rundunar Kwastam ta FOU a shiyyar A Jerry Attach, ya shaidawa Aminiya cewa mutumin da aka kama yana baiwa rundunar muhimman bayanan da za a kai ga kame ragowar wadanda suka yi aika-aikar, “Da zarar mun kammala binciken mu zamu mika shi ga hukumar da ya dace su ci gaba da binciken”. Ya ce, Hukumar ta Kwastam din tayi asarar jajjurtaccen jami’i mai himma da yawan kwazon aiki wato Yakubu Shu’aibu, “Hakika Hukumar zata yi kewar rashin Yakubu, jami’an mu sun je Gombe sun yi wa iyalan sa ta’aziyya tare da jajanta masu, jami’i ne mai kwazon aiki kuma kisansa da ‘yan fasakwabri suka yi ba zai raunana kwarin gwiwar mu wajan yaki da fasakwabri ba”.

A ranar Lahadin makon jiya ne ‘yan fasakwarin suka budewa jami’an rundunar wuta wadanda suka kwato shinkafar fasakwabri akan hanyar Idiroko a jihar Ogun, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Jami’in rundunar mai anini biyu Yakubu Shu’aibu.