✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama Dan sanda da mutum 5 da zargin laifin garkuwa a Kalaba

Rundunar sojojin Najeriya karkashin shirin Operation Skolombo a Kalaba babban birnin jihar Kuros Riba, sun kama wani jami’in dan sanda tare da wasu mutum biyar…

Rundunar sojojin Najeriya karkashin shirin Operation Skolombo a Kalaba babban birnin jihar Kuros Riba, sun kama wani jami’in dan sanda tare da wasu mutum biyar da ake zargi da laifin yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

A wata majiya da aka sakaya suna, na cewa da safiyar ranar Litinin ne aka kama jami’in Dan sandan ta hanyar bayanan sirri.

Rahotan ya kara da cewa, jami’in dan sandan da ake zargin ya mallaki fegi a cikin garin Kalaba. A yanzu haka yana hannun jami’an soji da ke barikin Eburutu a wajen garin Kalaba za a gurfanar da shi idan an kammala bincike.