✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan sandan bogi a Ibadan

An kama wani Sufeton ‘yan Sanda na bogi mai suna Adebisi Kayode mai shekara 34 da ya saba karbar kudi daga hannun mutane yana cewa…

An kama wani Sufeton ‘yan Sanda na bogi mai suna Adebisi Kayode mai shekara 34 da ya saba karbar kudi daga hannun mutane yana cewa zai taimaka masu sayan motocin gwanjo da Hukumar ‘Yan Sanda a Jihar Oyo take sayar wa mabukata a kan farashi mai rahusa.

Sashen Yaki da Fashi da Makami (SARS) ne ya kama wannan mutum wanda ya jinginar da sana’arsa ta walda ya kama yin sojan gonan ‘yan sanda a Ibadan.

Asirinsa ya tonu ne bayan yawaitar koken jama’a zuwa ofisoshin ‘yan sanda, wadda suka yi binciken da suka yi nasarar kama shi a Ibadan. Binciken ya nuna cewa Adebisi Kayode ya karbi kudi fiye da Naira miliyan 2 daga hannun mutane daban-daban da yake yi masu alkawarin taimaka masu samun sayan motoci da ‘yan sanda suke kada masu kararrawar gwanjo.

Da yake nuna mutumin ga ‘yan jarida, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Oyo, Abiodun Odude ya ce, a lokacin da aka kama shi an samu ankwa da bulala da wasu takardu a tare da shi da yake nuna wa mutane shaidar cewa shi dan sanda ne mai mukamin Sufeto, yana yi musu zamba cikin aminci.

Kwamishinan ya ce da zarar jami’ansa sun kammala bincike za su gurfanar da shi gaban kotu domin yanke masa hukumci. Ya shawarci jama’a su yi taka-tsan-tsan da irin wadannan mutane masu yi wa aikin dan sanda sojan gona. Ya ce ‘yan Sanda a Jihar Oyo suna yin tallar kada kararrawar gwanjon kayan da ta kama ne a cikin kafofin labarai domin sanar da mabukata.