✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama gurgu jagoran ‘yan kungiyar asiri da kullin tabar wiwi 300

Wani nakasasshe da ke hada-hadar tabar wiwi kana jagoran ‘yan kungiyar asiri a yankin Enu gada daura da Lafenwa a Abeokuta ya shiga komar ‘yan…

Wani nakasasshe da ke hada-hadar tabar wiwi kana jagoran ‘yan kungiyar asiri a yankin Enu gada daura da Lafenwa a Abeokuta ya shiga komar ‘yan sandan jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya cewa, a ranar Lahadin da ta gaba ta ne jami’an rundunar suka kama gurgun da kunshin  ganye 300 da ake zargin kunshin tabar wiwi ne.

DSP Abimbola, ya ce gurgun da suka kama mai suna Ibrahim Aremu, da ake wa lakabi da Jenromi ya shahara wajen jagorantar ‘yan kungiyar asiri da ke tayar da tarzoma a yankin, ya ce jami’an rundunar sun kai wa gungun ‘yan kungiyar asirin farmaki a yankin Enugada inda suka arce, sannan aka kame gurgun.