Da Dumi Dumi

An kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Hamisu Wadume

Hamisu Bala Wadume
Hamisu Bala Wadume

An samu labarin cewa an kama wanda ake zargi da satar mutane wanda kama shi ya yi sanadiyar mutuwar ’yan sanda uku a Jihar Taraba, Hamisu Wadume.
Kafar Premium Times ta ruwaito cewa an ga lokacin da aka shigo da Wadume Ma’aikatar Tsaro a Abuja, amma har yanzu jami’an tsaro ba su fitar da sanarwa ba.

Alhaji Hamisu Bala Wadume wanda a ’yan kwanakin nan labarinsa ya mamaye kakafen watsa labarai na gida da waje. Kafin kashe ’yan sanda uku da farin hula daya da ake zargin sojoji da yi a ranar 6 ga Agusta, jama’ar garin Ibbi ne kawai suka san labarinsa.

A saurari karin bayani.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya