✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama kocin Fyling Eagles a Landan

Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun ce ’yan sandan birnin Landan sun kama kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Matasa ta Najeriya Flying Eagles, Mista…

Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun ce ’yan sandan birnin Landan sun kama kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Matasa ta Najeriya Flying Eagles, Mista Paul Aigbogun saboda tayar da hankalin wata mata bayan ya yi tatil da giya.

Kocin wanda ke zaune da iyalinsa a Arewa maso Yammacin birnin Landan an ce a ranar Juma’ar da ta wuce da misalin karfe 6:00 na safe bayan ya sha giya sai ya nufi kofar gidan wata makwabciyarsa inda ya rika kiran sunanta yana fadin bakaken maganganu sannan ya bukaci ta bude masa kofa ko ya yi amfani da karfin tuwo wajen karya kofar.  Hakan ya sa matar ta rude ta rika ihu tana neman agajin makwabta su kuma suka sanar da ’yan sanda kafin a kama shi.

Binciken da ’yan sanda suka gudanar a kan Paul sun gano ya sha giya ce fiye da kimar da aka amince wani ya sha har ninki biyar a ma’aunin shan giyar, kuma hakan ya saba wa dokar birnin Landan.

Koci Paul Aigbogun ya taba horar da kulob din Warri Wolbes da Enyimba kafin ya zama kocin Fyling Eagles yakan ziyarci iyalinsa a Landan ne duk lokacin da ya samu hutu.  Mutum ne da ke yawan shan giya yan buguwa ya zama tamkar mahaukaci.

Rahotannin sun ce akwai yiwuwar Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta dauki mataki a kan kocin da zarar ya koma gida, ganin yadda ya zubar mutuncin kasar nan a idon duniya dalilin yawan shan giya.

Zuwa hada wannan rahoto ’yan sandan birnin Landan ba su bayyana hukuncin da suka yanke ga Paul ba, sai dai alamu sun nuna cewa akwai yiwuwar a daure shi tare da cin tararsa makudan kudi.