✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama lauya da cin zarafin ƙaramar yarinya

Wata lauya mai suna Tolu Olaoye da ke zaune a unguwar Baruwa a Legas ta shiga komar ’yan sanda, inda ake tuhumar ta da cin…

Wata lauya mai suna Tolu Olaoye da ke zaune a unguwar Baruwa a Legas ta shiga komar ’yan sanda, inda ake tuhumar ta da cin zarafin yarinya ’yar shekara 15 da ke yi mata aikace-aikace a gidanta.

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Legas, Edgal Imohimi ya sami labarin abkuwar lamarin ne bayan da aka sanya hoton yarinyar mai suna Abigail Opebiyi a yanar gizo, nan take ya ba da umarnin bincike har aka kai ga kame lauyar, aka kuma garzaya da yarinyar asibiti domin kula da lafiyarta, a sakamakon irin manyan rauni da lauyar ta yi mata a kanta da gwiwar hannunta da kuma sassa da dama na jikinta.

Kakakin rundunar ’yan sandan Legas, SP Chike Oti ya shaida wa Aminiya cewa an iza ƙeyar wacce ake zargin zuwa sashin binciken mata na rundunar ’yan sandan jihar, inda babbar jami’a a ɓangaren, SP Adejoke Cole ke bincikar wacce ake zargin. 

Haka kuma ya ce za a gurfanar da ita a kotu da zarar binciken ya kammala.