✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama limami da basarake da laifin garkuwa da mutane

‘Yan sanda masu yakar garkuwa da mutane sun kama wani limamin coci da maigarin Obor, bisa zargin kisan kai da garkuwa da mutane a Awara,…

‘Yan sanda masu yakar garkuwa da mutane sun kama wani limamin coci da maigarin Obor, bisa zargin kisan kai da garkuwa da mutane a Awara, Karamar Hukumar Oguta, Jihar Imo.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Imo, Isaac Akinmoyede, yayin gabatar da mutanen a hedikwatarsu da ke Owerri, ya zargi basaraken da faston da kashe jami’ai biyu na hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi (NDLEA).

CP Akinmoyede ya ce basaraken ya samar wa masu garkuwa da mutane motar da suke aikata laifin da ita, shi kuma faston yana jagorantar barayin.

Ya ce an kwace bindiga kirar AK47 da harsasai 120 da masu garkuwar suka kwace daga hannun jami’an NDLEA da wata da mora kirar Lexus SUV da sauran manyan laifuka.

Kwamishinan ya kara da cewa ‘yan sanda sun samu Naira miliyan hudu da dubu dari biyu daga cikin kudin fansar da ‘yan bindigar suka karba daga hannun wasu mutane.

Masu garkuwar sun kuma ba wa basaraken Naira miliyan uku daga cikin kudin fansa Naira miliyan bakwai da suka karba, saboda sun batar masa da motar da ya ba su su rika aiki da ita.

Basaraken ya amsa cewar bayan Naira miliyan uku da ‘yan fashin suka ba shi, suna biyan sa wasu kudade a duk lolacin da suka karbi kudin fansa.

Ya kuma ce yana sane da cewar ana yin amfani da motarsa ne a yi garkuwa da mutane.

Sauran mutanen da ake zargi sun hada da wani dan shakera 65 da wani mai 60 da da mai sherar 40 da dan shekara 38. Akwai kuma mai shekara 38 da wani dan shekara 32 da shekara 30.