✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ma’aikaciyar asibiti da wasu 4 da suka sace tagwaye a Kebbi

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS a jihar Kebbi, ta kama wata ma’aikaciyar asibitin Koyarwa na jami’ar Usman Danfodio Sakkwato da wasu mutum hudu…

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS a jihar Kebbi, ta kama wata ma’aikaciyar asibitin Koyarwa na jami’ar Usman Danfodio Sakkwato da wasu mutum hudu da ake tuhumarsu a kan sace wasu yara biyu a yankin Zuru da ke jihar.

Wadanda aka kama sun hada da: Ma’aikaciyar asibitin mai suna Helen Samuel da kuma Dorothy Okonkwo, Comfort Nwanko, Uchena Benedict da wani mai suna Moses daga jihar Anambra sauran daga jihar Delta.

Jami’an DSS sun yi nasarar kama wadanda ake zargin da sace yaran ne bayan iyayen yaran Yusuf Henso da Rabi Kabiru sun sanarwa da ‘yan bangar unguwar da bacewar tagwayen ‘ya’yansu.

‘Yan bangar unguwar ne suka sanarwa da jami’an DSS daga bisani suka fara bincike hakr aka samu nasarar kama mutanen da suka sace yaran.