✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mabarata 48 a Oyo

Gwamnatin Jihar Oyo ta kama mabarata 48 da ke yawon barace barace a kan hanyoyin birnin Ibadan. Wadanda aka kama sun hada da mata dauke…

Gwamnatin Jihar Oyo ta kama mabarata 48 da ke yawon barace barace a kan hanyoyin birnin Ibadan. Wadanda aka kama sun hada da mata dauke da goyon yara ’yan shekara daya zuwa biyu da kananan yara masu shekara 5 zuwa 7 da maza masu shekara 25 zuwa sama. Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa, mafi yawan wadanda aka kama sun fito yawon ci-rani ne daga garuruwan Arewa kuma da yawa daga cikinsu babu wata nakasa a jikinsu.

Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Oyo Hajiya Fausat Joke Sanni, ita ce ta jagoranci  jami’an duba-gari daga Ma’aikatar Tsabtace Muhalli zuwa Iwo Road da Mokola Round About da ke Ibadan inda aka yi wannan kame a ranar Alhamis din makon jiya.

Da yawa daga cikin mata masu goye da yara a bayansu sun yi ta kuka lokacin da jami’an suke tunkuda keyarsu zuwa cikin motar da ta kwashe su zuwa sansanin da aka tanadar masu a birnin Ibadan.

Kwamishinar ta ce, “Za a ci gaba da aiwatar da wannan tsari musamman a birnin Ibadan duk lokacin da aka hango irin wadannan mabarata a kan hanyoyi to za mu dawo kansu.” Ta ce, “Wannan sabon tsari ne da Gwamna Seyi Makinde, ya fito da shi domin kawar da kananan yara da mabarata daga yawon barace-barace a kan hanyoyi. Za mu killace su a sansanonin da muka tanadar musu da za a rika koyar da su sana’o’i domin kyautata rayuwarsu.”

Kwamishinar ta yi kira ga iyaye su taimaka wajen kyautata kula da rayuwar ’ya’yansu wajen hana su yawon bara a kan hanya. Kuma ta tunatar da iyayen yara game da burin gwamnatin jihar kan ilimantar da kananan yara a kyauta.

Aminiya ta zanta da wadansu mabarata da sabon shirin ya rutsa da su wadanda suka rika kuka suna cewa sun gwammace a kyale su koma garuruwansu na Arewa.