✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mafarauta da laifin kisan giwaye a Kuros Riba

Yanzu haka wasu mafarauta uku da ke kauyen Nsofang a karamar Hukumar Etung ta Jihar Kuros Riba za su dandana kudarsu sakamakon zarginsu da aka…

Yanzu haka wasu mafarauta uku da ke kauyen Nsofang a karamar Hukumar Etung ta Jihar Kuros Riba za su dandana kudarsu sakamakon zarginsu da aka yi na kashe wasu giwaye  guda uku. Doka ce mai tsanani a jihar ga duk wanda aka samu da laifin kama wani naman dawa da sunan farauta.
Majiyar Aminiya ta shaida cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a dajin kauyen  Edondong na karamar Hukumar Ikom.
Da yake karin haske kan lamarin, Mista Arikpo Ikom,  kwamishinan ma’aikatar kula da gandun daji da kare muhalli ta jihar, ya ce giwayen baki ne suka yiwo kaura  daga  dajin Tagamanda a Jamhuriyar Kamaru.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin mafarautan a ofishin ’yan sanda, amma hakan ya ci tura, kodayake mai magana da yawun rundunar, DSP John Imoh ya tabbatar da afkuwar lamarin.