✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai ba wa masu garkuwa da mutane sa’a

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce ta samu nasarar kama babban dan tsibbu da ake zargi da ba masu garkuwa da mutane sa’a a kokarin…

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce ta samu nasarar kama babban dan tsibbu da ake zargi da ba masu garkuwa da mutane sa’a a kokarin da take yi wajen magance matsalar garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin Hedkwatar ’Yan sandan Najeriya, Mataimakon Kwamishinan ’Yan sanda Frank Mba,  ce ta bayyana haka, inda ta ce ’yan sanda masu gano masu aikata miyagun ayyuka daga Sashin Daukin Gaggawa kan Ayyukan Sirri na Ofishin Sufeto Janar (IRT), wadanda Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Abba Kyari ke jagoranta da sauran jami’an da ke aiki a karkashin Shirin Yaki da ’Yan bindiga na Farmakin Kasa (Operation Puff Adder) sun kama wani mai suna Malam Salisu Abubakar, mai shekara 48, dan asalin Karamar Hukumar Dutsinma a Jihar Katsina da ake zargi da ba ’yan ta’addan sa’a.

Malamin da shi ne mai ba masu garkuwa da mutanen da suka addabi hanyar Abuja zuwa Kaduna da wasu sassa na Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya sa’a, an kama shi ne a ranar Talatar da ta gabata 16 gaAfrilu, sakamakon bin diddigin bayanan sirri da kuma kaddamar da farautar gano shi a maboyarsa da ke wani daji a kauyen Galadima da ke Jihar Kaduna.

Sanarwar ta ce: “Bincike ya samu wanda ake zargin da taimakawa da tallafa wa miyagun ayyukan fashi da makami da sace mutane ana yin garkuwa da su a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. Kuma wanda ake zargin ya kware wajen bayar da sa’a da tsibbace-tsibbace da bayar da bayanan sirri ga masu garkuwa da mutane kafin da kuma bayan sun aikata ta’asarsu.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Babu shakka kama shi za ta taimaka wa ’yan sanda wajen kamo masu garkuwa da mutane da dama da sauran masu aikata miyagun ayyuka da suka gudu.”

Har wa yau sanarwar ta ce a ranar 14 ga Afrilun baban an kama wani mai suna Godwin Ige da ake yi wa lakabi da ‘White’ a Abuja bisa zargin kasancewa mutum na hudu da suke da hannu a sacewa da yin garkuwa da ma’aikacin gidan talabijin na Channels Mista Friday Okeregbe.

Godwin Ige, mai shekara 28 dan asalin Karamar Akoko-Edo a Jihar Edo ’yan sanda sun same shi da bindiga kirar gida da harsasai masu rai 11 da mota kirar Honda Accord  mai Lamba KWL 420 GU wadda aka yi amfani da ita wajen sacewa da garkuwa da ma’aikacin a ranar 22 ga Maris din bana.

Sanarwar ta ce, Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya yana rokon hadin kan jama’a, tare da hakuri da nuna fahimta domin rundunar da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da aiki wurjanjan har sun tabbatar da gidaje da hanyoyin kasar nan sun kubuta daga ayyukan miyagu.