✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai safarar yara ya sayi jaririya Naira dubu 550

Hukumar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama mai safarar yara da laifin sayar da yarinya akan kudi Naira dubu 550. Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar…

Hukumar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama mai safarar yara da laifin sayar da yarinya akan kudi Naira dubu 550.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Anambra Haruna Mohammed, ya ce wanda aka kama ya shahara ne wajen sace jarirai da yara ya kuma sayarwa masu sayan yaran da aka sato.

Wanda ake tuhuma da wannan laifin mai suna Edith Ewudo da ke layin orsumoghu a unguwar Awada ya sayi jaririya akan Naira dubu 550 daga hannun wani mai suna Ndidi Egeonu a unguwar odume Obosi.

Yanzu da an mika Edith ga Kotu don yanke masa hukunci.