✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama makauniyar karya a Anambra

Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra ta kama wata mata mai suna Ngozi Dike, mai shekara 37 wadda take yawo da yara suna yi mata jagora…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra ta kama wata mata mai suna Ngozi Dike, mai shekara 37 wadda take yawo da yara suna yi mata jagora tana bara a matsayin ita makauniya ce, alhali ba makauniya ba ce.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra, SP Haruna Muhammed,  ya ce “An kama matar ce a Kasuwar Oye Olisa a yankin Ogbunike a Karamar Hukumar  Oyi.  “A ranar Asabar 15 ga Fabrairu nan, an kama wata mata mai suna Ngozi Dike tana yawo da yara suna yi mata jagora tana yawon bara a matsayin ita makauniya ce alhali babu wata larurar makanta tare da ita.” inji shi.

SP Muhammed, ya ce yaran masu suna Blessing Ezewanne mai shekara 8 ’yar garin Ugwuta da Fabour Ezeagu, mai shekara 11 daga garin Nwari, sai kuma wata Ohaji-Egbema daga Jihar Imo duk suna yi mata jagora a matsayin mabaraciya.

Ya ci gaba da cewa, “Binciken da muka yi ya nuna cewa matar ba ta da wata larura ta makanta tana yin haka ne domin neman kudi a hannun jama’a. Kuma Ngozi Dike, ta nemi izinin iyayen yaran biyu daga cikin masu yi mata jagora cewa za ta dauki dawainiyar karatunsu, amma sai take amfani da su zuwa kasuwanni don yin barace-barace

Jami’in ’yan sandan ya ce, da zarar sun gama bincike za su mika zuwa kotu don yi mata shari’a