Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An kama masu amfani da motar daukar marasa lafiya suna safarar kwayoyin Taramadol

Kwanturola Muhammed Abba Kura yana nuna wa ‘yan jarida kwayoyin Tramadol da aka kama a cikin motar daukar marasa lafiya
Kwanturola Muhammed Abba Kura yana nuna wa ‘yan jarida kwayoyin Tramadol da aka kama a cikin motar daukar marasa lafiya

Hukumar Kwastam ta Apapa a Legas ta kama mutum biyu da suka yi amfani da motar daukar marasa lafiya suka yi safarar kwayoyin Tramadol a yunkurinsu na ficewa da su daga cikin tashar jiragen ruwa ta Apapa.                                                                                                                                              Asirin direban motar mai suna Michael Ajibade da mataimakinsa Olatunde Emmanuel ya tonu ne lokacin da direban ya tuko motar a guje sanye jiniya inda ya yi kicibis da jami’an Kwastam a babbar kofar shiga tashar inda binciken kwakwaf ya bankado wannan lamari.

Da yake nuna mutanen da motar tare da kwayoyin Tramadol ga ’yan jarida, Kwamandan Hukumar Kwastam ta Apapa Kwanturola Muhammed Abba Kura ya ce, “Muna ci gaba da tsare mutanen da muka kama cikin dare ranar Juma’a makon jiya. Mun gano motar daukar gawar tana dauke da katan 10 na kwayoyin Taramadol da kudinsu ya kai Naira miliyan 2 da dubu 800. Za mu ci gaba da bincike domin gano ko akwai hannun jami’anmu wajen fasa kwantainar da ba mu riga mun tantance ta ba da ke dauke da katan 211 na Tramadol da kudinsu ya kai Naira miliyan 59 da aka shigo da su daga kasar Indiya.”

ADVERTISEMENT

Ya ce ana zargi wadansu da fara sace wasu daga cikin kwayoyin daga cikinta, inda ya ce, duk wanda aka same shi da hannu a wannan lamari zai mika shi ga hukuma. Ya ce “Duk jami’in Kwastam da ke aiki a karkashina idan ya san yana da hannu a wannan al’amari to kada ya kuskura ya kusance ni domin kamun kafa ko neman alfarma don ba zan taba amincewa a yi amfani da ni wajen yin zagon kasa ga kasar nan ba.”

Ya ce, duk wanda aka samu da hannu wajen shigo da wadannan kwayoyi masu sa maye wadanda aka yi dabarar lullube su a karkashin halattattun magunguna domin bad-da-kama da wadanda suka bude kwantainar kafin a tantance ta za su dandana kudarsu. Ya ce, za a gurfanar da wadanda ake zargi gaban kotu bayan kammala bincike.

ADVERTISEMENT