Aminiya

An kama masu sayarwa ‘yan fashi makamai da albarusai dubu 10

‘Yan Sandan Oyo sun kama mutane 4 dauke da albarusai dubu 10 da suke dillancin sayarwa ga ‘yan fashi da makami.

An yi nasarar kama su ne a maboyarsu da ke unguwar Oke-Bola a birnin Ibadan. Haka kuma ‘yan sandan sun nuna wasu ‘yan mata 2 masu shekaru 20 zuwa 22 da aka same su da bindiga da harsashi guda 1 da suka ce suna yi wa samarinsu ‘yan fashi da makami aikin jigilar bindigogi da boyewa daga Legas zuwa Iseyin a Jihar Oyo ne.

ADVERTISEMENT
‘Yan mata biyu da aka kama dauke da bindiga a tare dasu a Ibadan.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo CP Shina Olukolu ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a lokacin da yake yi wa manema labarai bayani tare da nuna masu wasu mutane 11 masu damfarar mutane ta hanyar yin amfani da takardu masu dauke da tambarin kamfanin STAAGMART da Bankin bayar da rancen kudi ga kananan ‘yan kasuwa (micro finance) da ke Oyingbo a Legas. Bayan fatattakar su daga Lokoja a Jihar Kogi a inda suke gudanar da danyen aikin nasu sai suka isa birnin Ibadan suka sauka a Otal din S.L HOTEL da ke sashen Boluwaji a birnin Ibadan a inda ‘yan sanda suka yi masu dirar mikiya suka kama su duka in ji Kwamishinan. Ya ce, da zarar sun kammala bincike zasu gurfanar da su mutanen da aka kama ake zargin su da aikata miyagun ayyuka gaban kotu domin yanke musu hukuncin da ya yi daidai da laifin su.

Wani bangare na mutane 11da aka kama da zargin damfarar mutane.
ADVERTISEMENT