✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu sayen kuri’u a Kano

Sakamakon bayyana zaben gwamna a Jihar Kano da Hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta yi a matsayin wanda bai kammala ba wanda kuma ya janyo…

Sakamakon bayyana zaben gwamna a Jihar Kano da Hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta yi a matsayin wanda bai kammala ba wanda kuma ya janyo za a sake gudanar da zabe a wasu rumfunan zabe da suka kai 172 hakan ya janyo ’yan siyasa a jihar sun fara sayen kuri’u don cikar burinsu na ganin cewa sun sami nasarar cin zabe.

A yanzu haka dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa ta kama mutanen da take zargi da sayen katin zabe a Unguwar Gama da ke yankin Karamar Hukumar Nassarawa cikin Jihar Kano.

Da yake bayani ga manema labarai Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya bayyana cewa an kama mutanen a wurare daban-daban a cikin jihar, inda suka hada da Unguwar Gama da DSP Haruna Abdullahi ya bayyana cewa jami’ansu na ofishin Gwagwarwa ne suka kama mutanen, wadanda suka hada da Sa’adatu Isma’il mazauniyar Unguwar Birged da Hajiya Halima Abba mazauniyar Unguwar Tal’udu, inda suke shiga gidaje suna sayen katin zabe daga hannun al’ummar yankin.

“An kama matan da katin zaben da suka riga suka saya kimanin 10 sai kuma tsabar kudi Naira dubu 10 a hannunss, wanda suke niyyar ci gaba da sayen katin zaben da su”

Har ila yau ’yan sandan sun ce sun kama wasu matasa biyu a unguwar ta Gama wadanda ake zargin suna kokarin sayen katin zaben a hannun jama’a, lamarin da ya sa ’yan sandan suka kwace su da kyar daga hannun fusatattun matasan yankin.

Haka kuma rundunar ta kama wani mutum mai suna Mukhtar Shu’aibu wanda ake kira da Ustaz a yankin Dandinshe Gabas inda yake bi yana sayen katin zabe a hannun jama’a, wanda aka kama din ya yi ikrarin cewa ya sayi katin zabe guda biyu a kan Naira dubu uku kowanne.

Kakakin ya bayyana cewa rundunar ta fara bincike a kan lamarin kuma da zarar ta kammala za ta gurfanar da wadanda ake zargi gaban kuliya.

A wani labarin kuma Rundunar ’Yan Sandan ta Kano ta musanta jita-jitar da ke yawo, musamman a kafafen sada zumunta na intanet, cewa an canza Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar Kano, Muhammad Wakili; inda aka mayar da shi Jihar Zamfara.

Yayin da yake zantawa da manema labarai Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya bayyana labarin da ake yadawa a matsayin kanzon kurege saboda ba shi da tushe ballantana makama. “Wannan magana ta canja wa Kwamishinan wurin aiki karya ce, wacce wasu suka kirkira don cin ma wata manufa tasu ta kansu. A iya sanina Kwamishina Muhammad Wakili har yanzu shi ne Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano.”