Search
Subscribe
An kama masu yunkurin juyin mulki a Ghana

An kama masu yunkurin juyin mulki a Ghana

Dakarun gwamnatin Ghana sun dakile wani yunkurin juyin mulki a fadar Shugaban Kasar.

Jami’an tsaron kasar sun tsare wadansu mutum uku da dimbin makamai a wani samamen hadin gwiwa da aka yi ranar Juma’a, kamar dai yadda Ma’aikatar Labaran kasar, ta sanar.

Ma’aikatar ta ce hukumomin tsaron sun gudanar da aikin ne bayan wata 15 ana tattara hujjoji tare da bin diddigin manyan wadanda ake zargi.

Sanarwar da ma’ikatar ta fitar ta ce daya daga cikin mutanen da ake tsare da su din mai kera makamai na cikin gida ne.

Masu yunkurin juyin mulkin sun shirya karbe ikon wasu muhimman wurare da kuma samo kudin da za su yi amfani da su wurin kifar da gwamnatin kasar, a cewar sanarwar.

Gwamnatin kasar na zargin daya daga cikin mutanen da hada baki da wadansu jami’an sojin kasar kan yadda za su yi juyin mulkin da inda za su samu makamai a tsakanain watan Yuni zuwa Agustan bara, inji sanarwar.

Ghana na cikin kasashen Afirka ta Yamma da ba a samun rikici wurin mika mulki tunda kasar ta fara amfani da tsarin jam’iyyu da yawa a 1992.

A watan Dismaban 2016 Shugaba Nana Akufo-Addo ya lashe zaben kasar inda ya kayar da Shugaba mai ci na wancan lokaci John Mahama wanda ya amince an kayar da shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin