✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matar da talauci yasa ta jefa danta a masai a Ogun

Wata matar aure mai shekaru 30 mai suna Risikat Olabintan ta shiga komar ‘yan sanda a jihar Ogun bayan da aka same ta da laifin…

Wata matar aure mai shekaru 30 mai suna Risikat Olabintan ta shiga komar ‘yan sanda a jihar Ogun bayan da aka same ta da laifin jefa jaririn da ta haifa a masai.

Mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya shaidawa Aminiya cewa, matar da ake zargin da ke zaune a yankin Owode-Yewa, ta jefa yaron da ta haifa a masai ne jim kadan da haihuwarsa, “Wasu yara da ke wasa a harabar gidan ne suka jiyo kukan jaririn a daga cikin ramin masan lamarin da ya sanya suka an karar da jama’ar garin wadanda suka sanar mana nan ta ke muka garzaya muka ceto yaron.” In ji shi.

Ya ce, matar ta shaida cewa ita ta haifi yaron wanda shi ne haihuwar ta na shida, duba da yanayin talauci da take fama da shi sakamakon guduwar da mijinta ya yi ya barta da alhakin kulawa da ‘ya’yan sai ta yanke shawarar ta jefa yaron a masai ta ce tayi hakan ne da sanyin safiyar ranar da ta haife shi.

DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce zuwa yanzu ana kula da yaron da mahaifiyarsa a asibiti kafin daga bisani a ci gaba da bincike.