✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matashi da ya yi yunkurin sace yaro a makarantar Islamiyya

A yammacin ranar Asabar din nan ne dubun wani matashi ya cika wanda ya yi yunkurin sace wani yaro dan karami akan hanyarsa ta komawa…

A yammacin ranar Asabar din nan ne dubun wani matashi ya cika wanda ya yi yunkurin sace wani yaro dan karami akan hanyarsa ta komawa gida bayan an tashi daga makarantar Islamiyya a garin  Rigasa jihar Kaduna. 

Matashin wanda tuni aka mika shi ga kungiyar JTF da ke Titin Makarfi a Rigasa Kaduna ya tabbatar da cewa, wani abokin mahaifin yaron ne ya aike shi ya dauko masa shi a makaranta.

A cewar wata mazauniyar unguwar mai Suna Hajiya ta shidawa Aminiya cewa, Matashin ya yi yunkurin dauke yaron ne da nufin yin garkuwa da shi.

.” Sai Allah ya sa matasa‎ da ke wajen suka kama shi suka kuma mika shi ga yan JTF. Kuma yana can yana masu bayani domin ya ce, wai abokin mahaifin yaron ne ya aiko shi ya dauko masa shi. An aika da sako wajen iyayen da su je ofishin JTF din, in ji ta.

Haka shima a cewar, wani wanda ya samu zuwa wajen ya shaidawa Aminiya cewa, an mika wanda ake zargin ga ‘Yan Sandan Najeriya.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yakubu Sabo, ya ce bai samu labarin aukuwar lamarin ba daga wajen DPO na yankin.

Amma ya bayyana cewa zai yi bayani da zarar ya samu cikakkiyar abin da ya faru.