An kama matashi kan yi wa wata fyade a Ebonyi

Rundunar ’Yan sandan Jihar Ebonyi ta kama wani matashi da ake zargin makiyayi ne mai suna Laulo Isa, mai kimanin shekara 20 bisa zargin yi wa wata mata mai suna Mary Okereke fyade, lamarin da ya janyo mutuwar matar. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Awosola Awotinde, ne ya tabbatar wa manema labarai kama matashin.

Wata majiya ta kusa da marigayiyar ta shaida wa manema labarai cewa, lokacin da matar take dawowa daga wani kauye ne wanda ake zargin ya rika bin ta ya yi mata fyade a Unguwar Ufuezeraku Ugwulangwu da ke Karamar Hukumar Ohaozara da misalin karfe 8:00 na dare, lamarin da ake zargin ya yi sanadiyyar rasuwar Mary Okereke.

Ofishin ’yan sanda na Ohaozara ya shaida wa wakilinmu cewa, sun ga alamun ya yi kokawa da ita kafin ya ci karfinta, inda aka tsinci hularsa da takalmansa a wurin inda matasan kauyen suka bazama nemansa suka kama shi.

Aminiya ta ji ta bakin wanda ake zargin inda ya ce, “Sunana  Laulo Isa, kuma ni dan asalin Jihar Nasarawa ce neman kudi ya kawo ni Jihar Ebonyi. Babu shakka na sha giya na bugu ina hanyar dawowa gida  ne na hadu da wata mace tana tafiya na nuna mata bukatar ina so mu yi lalata, ita kuma daga nan sai ta fara zagina ni kuma na rama,  muka fara zage-zage na kamata da kokawa na kayar da ita, kuma tana kokarin ture ni domin ta tsira gaskiya lokacin a buge nake da giya.”

Ya ce yana cikin yi mata fyade sai ya ga wani yana wucewa da ya ji motsinsu ya haska su da tocila sai ya tsorata ya gudu, “Amma ban buge ta da makami ba, na dai yi lalata da ita sau daya kafin wani ya haska mu in gudu,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Matashin ya bayyana nadama kan abin da ya aikata inda ya ce, “Ban ji dadin abin da na yi ba, na yi nadama sharrin Shaidan ne na tuba ba zan kara ba.”

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya