✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matashi kan zargin satar fatari a Jigawa

Kotun Majistare da ke Dutse ta tsare wani matashi dan shekara 23 mai suna Yabo Ibrahim a gidan yari saboda zarginsa da satar fatarin wata…

Kotun Majistare da ke Dutse ta tsare wani matashi dan shekara 23 mai suna Yabo Ibrahim a gidan yari saboda zarginsa da satar fatarin wata mace.

Ana zargin ya saci fatarin matar ce a kauyen Yalwa da ke Karamar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa. Bayan an gurfanar da shi a kotun, an tuhume shi da laifin shiga gidan mutane ba da izini ba da kuma satar fatarin matar.

Matar da ta yi karar, ta ce sau da yawa idan ba ta nan, ana shiga gidanta, ana yi mata sace-sace. Ta ce da abin ya yi yawa ne sai ta fada wa makwabta da ’yan sanda, shi ne aka sa ido har aka kai ga kama wanda ake zargin.

Daga cikin kayan da aka kama matashin ya sata sun hada da rigar mama biyar da fatari guda bakwai da rigunan mata guda biyu, wadanda aka yi kiyasin kudinsu a kan Naira dubu bakwai.

Da aka gurfanar da wanda ake tuhumar gaban kotu, ya bukaci kotun ta yi masa adalci kuma ta sassauta masa wajen yi masa hukunci. Ya ce ya saci kayan ne saboda yunwa da yake ji kuma babu yadda zai yi wajan ciyar da kansa.

Alkalin Kotun Mai sharia Muhammed Lamin Usman ya umarci a tsare matashin a gidan maza na tsawon mako biyu kafin kotun ta gama nazarin irin hukuncin da ya dace a yanke masa.

Ya ce laifin da ake tuhumarsa ya saba wa sashi na 346 na Kundin Shari’a na Jihar Jigawa. Ya kuma dage sauraren shari’ar zuwa 12 ga watan gobe.