✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 5 na yunkurin kashe almajiri domin tsafi

An kama wadansu matasa biyar a garin Kona da ke Karamar Hukumar Jalingo a Jihar Taraba bisa zargin yunkurin hallaka wani almajiri dan shekarab 10…

An kama wadansu matasa biyar a garin Kona da ke Karamar Hukumar Jalingo a Jihar Taraba bisa zargin yunkurin hallaka wani almajiri dan shekarab 10 mai suna Nuhu, domin yin tsafi da sassan jikinsa.

Matasan da ake tuhuma, an kama su ne a bayan garin Kona, lokacin da suke kokarin kashe almajiri mai sana’ar yankan farce.

Kamar yadda wakilinmu ya binciko, daya daga cikin wadanda aka kama ne ya dauki almajirin daga Unguwar Mayo Dasa zuwa garin Kona da nufin zai yanke wa maigidansu farce. Daga nan ne ya wuce da  shi zuwa bayan garin Kona, inda wadanda ake zargi suke gudanar da ayyykansu na tsafi, ta hanyar hallaka bayin Allah.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an kai almajirin gaban shugaban matsafan, inda daya daga cikinsu ya sara masa adda a keya da nufin ya kashe shi. Amma da yake kwanansa na gaba sai ga wadansu mutane, wadanda nan take suka isa inda matsafan suke neman hallaka almajirin.

Majiyar ta ce ganin yadda yaron ke cikin jini sanadiyyar sararsa da adda da matsafan suka yi a keya, sai mutanen suka yi ihun neman dauki kuma a cikin  kankanen lokaci jama’ar garin suka hallara; inda aka kama su aka kai su gidan Sarkin Kona.

Sarkin Kona, Mista Augustine Njemang Benkam ya shaida wa Aminiya cewa ya yi bakin cikin kasancewar masu hallaka bayin Allah da sunan tsafi a masarautarsa. Ya ce ba zai amince wadansu batagari su lalata masa masarauta ba, saboda haka zai sa a ladabtar da wadanda aka kama sannan ya mika su ga jami’an tsaro na Sibil Difens, domin a ci gaba da bincikensu kuma a kai su kotu don a hukunta su.

Sarkin Kona ya bayyana cewa ba garin da zai ci gaba in ba zaman lafiya kuma dole ne iyaye su tashi tsaye su sa ido a kan ’ya’yansu domin hana su shiga ayyuka marasa kyau.

Ya ce wannan lamari na kama bayin Allah ana kashewa da sunan tsafi, sabon abu ne a Masarautar Kona kuma ba zai goyi bayan duk wanda aka samu da irin wannan laifi ba.

Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa an gano kawunan mutane masu yawa a inda matsafan ke aikata mummunan ayyukansu na tsafi a bayan garin Kona. Majiyar ta kara da cewa, wadanda aka kama sun dade suna hallaka bayin Allah, musamman kananan yara masu talla da masu wankin takalma da sauransu, inda suke yaudararsu, su kai su inda suke yin tsafi su hallaka su.

Idan za a tuna wata biyu da suka gabata a garin Yalwan Tau da ke Karamar Hukumar Jalingo, an kashe wadansu ’yan asalin Jihar Jigawa su uku, a cikin gonar shinkafa; inda aka yanke kawunansu aka tafi su.

Kwamandan Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Taraba, Alhaji Aliyu Ndanusa ya tabbatar da kama matasan biyar kan tuhumarsu da laifin ayyukan asiri a garin Kona da ke Karamar Hukumar Jalingo.

Ya ce wadanda ake tuhumar, an kama su ne a bayan garin Kona, a daidai lokacin da suke kokarin hallaka wani almajiri dan shekara10 da nufin yin tsafi da sassan jikinsa. Ya ce wadanda ake tuhumar sun hada da; Bruno Augustine da Pius Daniel da Elijah Daniel da  Destiny Dabid da John Gobai.

Alhaji Aliyu Ndanusa ya kara da cewa an kai yaron da aka kubutar daga hannun wadanda ake tuhumar zuwa Babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Jalingo, domin yi masa jinya. Ya ce hukumar ta kammala bincikenta a kan wadanda ake tuhumar kuma ta samu bayanai masu yawa dangane da ayyukan matasa na tsafi, don haka an tura su kotu don a yi musu shari’a.

Ya ce hukumarsa za ta ci gaba da sa ido don dakile ayyukan batagari a Jihar Taraba.