Search
Subscribe
An kama mutum 6 da ake zargi da kisan Agom Adara

An kama mutum 6 da ake zargi da kisan Agom Adara

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS reshen jihar Kaduna sun kama mutum shida da ake zargi da kisan Sarkin Adara, Agwom Adara, Maiwada Galadima.

Hukumar ta kama daya daga cikin shahararren mai garkuwa da jama’a Musa Mohammaed wanda ya addabi al’ummar jihar.

Daraktan Hukumar Mahmud Ningi ya ce a yanzu haka an kama mutum 20 da ake zargi da yin garkuwa da jama’a da kuma kisan sarkin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin