✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ‘Sarkin Aljanu’

A ranar litinin da ta gabata ce ’yan sanda suka gurfanar da wani da ake zargin ya shahara wajan damfarar jama’a da karbe abin hannunsu…

A ranar litinin da ta gabata ce ’yan sanda suka gurfanar da wani da ake zargin ya shahara wajan damfarar jama’a da karbe abin hannunsu da sunan shi Sarkin Aljanu a gaban kotu.

Mtumin mai suna Suleiman Umar mai shekara 37 wanda aka gabatar da shi a gaban Babbar Kotun Majistare da ke kofar Fada, Zariya ana zarginsa ne da damfarar mutane ta hanyar buga musu waya yana bayyana cewa shi Sarkin Aljanu ne.

Suleiman Umar dan asalin garin Kace da ke karamar Hukumar Lafai a Jihar Neja, yana zaune ne a Layin Dattawa, Hayin Ruwa Rigasa, Kaduna.

A ranar Talata da misalin karfe 11:00 na rana wani mai suna Suleiman Muhammed da ke zaune a gida Mai lamba 37  a Unguwar Liman cikin birnin Zariya, ya kai kara gaban DPO Kasim Abdul da ke ofishin ’yan sanda na kofar Fada cewa wani da ya saba damfararsa da sunan shi Sarkin Aljanu ne ya kira shi a waya cewa ya kai masa Naira dubu 450 ya ajiye masa a gidin wata itaciya a Madaci da ke kan hanyar Karau-Karau. Nan da nan ’yan sanda suka yi shigar burtu Allah Ya ba su sa’a suka kama shi. 

Bayan kammala bincike ne aka tura shi kotun domin ya fuskanci shari’a, inda mai gabatar da kara Sufeta Sarki Abdullahi ya ce ana tuhumar Suleiman Umar da yin barazana da cuta da sunan shi Sarkin Aljanu ne wanda hakan ya saba wa sashi na 377 da 307 na dokokin aikata manyan laifuffuka na Jihar Kaduna.

Wanda ake tuhumar ya amsa wasu daga cikin laifuffukan da ake zarginsa inda ya ce lallai ya sha damfarar wanda ya kai shi kara domin tsawon lokacin da suka fara hulda ya damfare shi har Naira dubu 65, sai dai bai amince da cewa ya yi wa wanda yake damfarar barazana ba.

Alkalin Kotun, Majistare Umar Bature, ya ce tunda wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa ba tare da wata gardama ba don haka a karkashin sashi na 157 na sabon kundin laifuffuka na Jihar Kaduna na shekarar 2017 ya yanke masa hukuncin zama gidan yari na tsawon shekara 10 ko zabin biyan tarar Naira dubu 200, kamar yadda sashi na 307 na manyan laifuffuka ya kunsa.

Aminiya ta tattauna da wanda ake tuhuma, a kan hanyarsa ta zuwa gidan yari cewa, “Na koyi wannan muguwar sana’ar ce a hannun wani maigidana da ya rasu, kuma muna sana’ar ba da magungunan Musulunci ne (Islamic Medicin), to ta nan na fara, kuma na kwashe tsawon shekara biyar ina gudanar da damfara da sunan ni Sarkin Aljanu ne ta hanyar buga wa mutane waya.”

Ya kara da cewa: “Wadansu suna amincewa tare da imani da abin da nake gaya musu wadansu kuwa har zagina suke yi. Ina shake muryata domin ina iya yin murya iri daban-daban, idan na shake muryata nakan yi muryar Sarkin Aljanu da na Galadiman Aljanu da na dan Autan Aljanu,  har da kukan awaki da na kyanwa da na jariri duk ina yi, kuma zai yi wuya ka gane. To haka nake yi idan mutum ya amince da ni sai in yi ta karbar abin hannunsa bai ganewa. Kuma a gaskiya na kwashe kusan shekara biyar ina wannan muguwar sana’a ta damfarar mutane da sunan ni Sarkin Aljanu ne, ina cewa zan ba su sa’a, ko zan yi musu kudi, ko zan bai kwa mace haihuwa, haka nake yi har in samu sa’a.  Shi kuma wannan na samu lambar wayarsa ce a wajen abokina mai suna dan Sarki. Mazaunin garin Bauchi, kuma shi Suleiman na kai tsawon shekara daya ina kiransa a waya, na fako ya turo mun katin waya na Naira dubu uku, sai kuma kudi Naira dubu 65 na karba daga gare shi, kuma wannan karon da na ce ya kawo rabin abin da ya mallaka zan gauraya in yi masa kudi ne sai asirina ya tonu.”

Sarkin Aljanun ya kara da cewa, “A wannan damfara da nake yi na samu sa’ar wani mutumin Neja inda na samu Naira dubu 200 a dunkule, sai kuma kananan kudi kamar Naira dubu 50 da sauransu, kuma a gaskiya duk cutar da na ta yi wa jama’a ba ni da komai sai fili kwata a Hayin Ruwa, Rigasa, kuma na yi nadama kuma ina rokon afuwa.”