✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama sigarin Dala 10m da aka yi fasakwauri a China

Hukumomi a Kudancin kasar Chaina sun kwace taba sigari ta kusan Dalar Amurka miliyan 10.6 da aka yi fasakwaurinta zuwa kasar. Jami’an tsaron gabar Teku…

Hukumomi a Kudancin kasar Chaina sun kwace taba sigari ta kusan Dalar Amurka miliyan 10.6 da aka yi fasakwaurinta zuwa kasar.

Jami’an tsaron gabar Teku ne suka kama kayan tabar ranar litinin kamar yadda rundunar tsaro ta Guangdong ta tabbatar.

Rundunar ta ce dakarun sun ya da zango ne a birnin Zhanjiang don dakile zirga-zirgar wani babban jirgin ruwa a ranar 6 ga watan Nuwamba a ruwan da ke kusa da yankin Qiongzhou.

Bayan sun karbe ikon jirgin da kwace tabar da aka yi safara, an gano kusan nau’uka 26 na tabar da aka san’anta a Chaina da wasu kasahe.

Tuni dai aka cafke wanda ake zargi da fasakwaurin don fadada bincike kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Wannan shi ne kayan taba sigari mafi yawa da dakarun tsaron gabar teku suka taba kamawa idan aka kwatanta da kayan da ake siyowa don kasuwanci daga kasashen duniya.

Jami’an tsaron Guangdong sun bayyana aniyarsu ta kai samame a dukkannin iyakokin ruwa don fadada binciken kan irin kayayyakin da ake safarar su don tabbatar da tsaro da sanyan idanu kan kayan da aka halatta shigo da su China ta ruwa.