Daily Trust Aminiya - Ya hada baki an yi wa kanwarsa fyade
Subscribe

Ya hada baki an yi wa kanwarsa fyade

An kama wasu samari da suka boye wata budurwa mai shekara 14 suna ta yi mata fyade har sai da dubunsu ta cika.

’Yan sanda a Jihar Bauchi sun cafke matasan su hudu da suka boye yayinrar a wani gida da suke ta saduwa da ita a unguwar Nasarawa da ke Karamar Hukumar Misau ta jihar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta bayyana haka ne yayin gabatar wa ’yan jarida wasu mutum 20 da ta kama bisa zargin aikata fyade a sassan jihar.

Kakakin Rundunar, DSP Ahmed Mohammed Wakili, ya ce matasan “suna ta saduwa ta ita na kusan wata guda. An kai ta Babban Asibitin Misau a duba ta, su kuma sun amsa laifin yayin da ake bincike domin a kai su kotu nan ba da jimawa ba”.

A Azare kuma an kama wani magidanci da ya yi wa diyarsa budurwa mai tabin hankali fyade a dakin uwarta, ya kuma amsa cewa ya yaudare ta ne da kudi.

Rundunar ta kuma damke wani matashi da ya hada baki da abokansa suka yi wa kanwarsa fyade da karfin tsiya a cikin motarsa, a garin Bauchi.

An kuma cafke wani mutum bayan ya yi wa wani yaro mai shekara 11 fyade da hanyar ludu a garin na Bauchi, inji rundunar.

DSP Wakili ya ce an damke wani mutumin da ya tare wata matar aure ya yi mata barazana ga rayuwarta cewa ta ba shi kudi N100,000, da ta ce ba ta da su ya yi mata fyade da karfin tsiya.

An kuma kama wasu matasa hudu da suka yi wa wasu ’yan mata ya da kanwa fyade a lokacin da suka yi tafiya zuwa kauyen Sabon Kaura.

’Yan sandan sun kuma cafke wasu mutum uku da suke yi ta wata karamar yarinya mai shekara tara fyade a yankin Gamawa na jihar.

Kakakin ‘yan sandan ya ce matasan sun amsa laifin yayin da ke ci gaba da jinyar yarinyar.

Ya ci gaba da cewa rundunar ta kuma kama wani mutum da ya yaudari wata yarinya mai shekara 13 da kwai da mangwaro a Ningi, ya yi mata fyade a cikin shagonsa na dinki kuma yarinyar ta dauki ciki.

Rundunar ta ce tana bincike kan wani wanda ake zargi da yunkurin yi wa wata karamar yarinya ’yar shekara shida fyade a garin Dass.

Ta ce dukkannin wadanda ake zargin an yi wa fyaden suna samun kulawa a asibiti yayin da bincike ke wakana domin tabbatar da karin hujjoji kafin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

texem
More Stories