✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wadanda suke fashi a Dambam da masu yada bidiyon karya

Rundunan ’Yan sandan Jihar Bauchi ta kama mutum uku da take zargi da fashi a hanyar Kano zuwa Maiduguri a kusa da kauyen Bam da…

Rundunan ’Yan sandan Jihar Bauchi ta kama mutum uku da take zargi da fashi a hanyar Kano zuwa Maiduguri a kusa da kauyen Bam da ke Karamar Hukumar Dambam da ke jihar tare da mutum biyu da take zargi da yada faifan bidiyon da ke zargin cewa ’yan sanda ne ke aikata fashi da makami a yankin da kuma mutum biyu da take zargi su ne suka zanta da gidan rediyon Amurka wanda ya yayata zargin ’yan sanda da fashin.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi Mista Philip Maku ne ya shaida wa ’yan jarida haka a Bauchi lokacin da yake gabatar da wadanda ake tuhumar, inda ya ce bincken da ’yan sanda suka yi ne ya kai su ga kama Shehu Abdullahi mai shekara 20 da Babawuro Jauro mai shekara 27 da Wada Wakil Musa mai shekara 25 da ake zargi da fashi da makamin da aka zargi ’yan sandan da aikatawa.

Ya ce wadannan mutum uku ne suka hada kai da wadansu mutum bakwai da har yanzu ba a same su ba, suka rike miyagun makamai suka rufe hanyar Maiduguri zuwa Kano suka tsare wata mota kirar Sharon mai lamba DA 300 ABS da ke dauke da fasinjojin da suka fito daga Kebbi zuwa Maiduguri suka yi musu fashi.

’Yan sandan sun ce sun same su da babur kirar Kasea da bindiga mai baki biyu da sanduna 7, da diga shida da adda bakwai da kwari da baka  uku da kibiyoyi 194 da karafa masu tsini 10 da wukake shida da harsasai da makullin babur daya da lambar babur da wayoyi  uku, da layin wayoyi 20 da zannuwa 25, da takalma bakwai da huluna 33, da sauransu.

Kwamishinan ya ce sun kama Bala Mato mai shekara 57 da Mohammed Bappa Yerima mai shekara 59, inda suke zargin Bala Mato ne ya zanta da gidan Rediyon Amurka yana cewa ’yan sanda ne suka rufe hanyar suka yi fashin, alhali ba ya wajen da abin ya faru. Kuma ya janye kalaman da ya yi a gidan rediyon ya wanke ’yan sanda. Shi kuwa Yarima ya rubuta a Facebook cewa ’yan sanda ne ke aikata fashi da makami a yankin da nufin tunzura jama’a.

Da yake zantawa da manema labarai Bala Mato ya ce ya ji mutane na fadin haka ne shi ma ya fada, yana rokon gafarar ’yan sandan.

Daya daga cikin mutanen da ake zargi da aikata fashin, Wada ya shaida wa manema labarai cewa su ne suka yi fashin.