Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An kama wanda ake zargi da kashe mahaifinsa a Abuja

Hukumar ‘yan sanda a Abuja tana tuhumar saurayi mai suna Huzaifa Hussaini Usman dan shekara 22 akan zargin kashe mahaifinsa Alhaji Hussaini Usman wanda ke kasuwanci da kuma aikin kwangila a gidansa da ke rukunin gidaje na Abdulkareem Adisa a unguwar Apo, Abuja.

Tun a ranar 28 ga Oktoba 2018, ‘yan sandan suka fara binciken kisan, inda suka gano wanda ake zargi da aikata kisan Hussaini Usman dan sa ne.

ADVERTISEMENT

A lokacin da aka aikata kisan an ta yada rahoton cewa, ‘yan fashi ne suka shiga cikin gidan Hussaini Usman suka kashe shi.

ADVERTISEMENT