Da Dumi Dumi

An kama wanda ya auri mata 60 a cikin shekara 25

Jami’an ’yan sandan ofishin Purbadhala da ke Gundumar Mymensingh a kasar Bangladesh sun kammala hada rahoto kan karar da wata matar aure mai suna Rosy Khanum ta kai ofishin a kan mijinta bisa zargin ya aure ta a matsayin mata ta 60 da ya aura cikin shekara 25.

Bayan korafin matar ’yan sandan sun tsare mijin nata mai suna Abu Baker, mai shekara 45. A cewar ’yan sandan sun kama shi ne saboda auren mata 60 da ya yi a cikin a shekara 25 ta amfani da takardun bogi da sunan karya da yaudarar matan.

Abu Baker dan Badshah Mia daga kauyen Shobharchar yana Unguwar Goyalerchar a Gundumar Jamalpur.

An kama Abu Baker a daren ranar Lahadin da ta gabata.

Abu Baker malamin makaranta ne a yankinsu, ya yi auren farko ne lokacin da yake da shekara 20, yanzu ya auri mata 60 ke nan yana da shekara 45, yayin da yake amfani da takardun bogi da ke nuna cewa bai taba yin aure ba ko shi gwaro ne da sauran rubutun bogin da ya yi a takardunsa.

ADVERTISEMENT

A watan Agustan da ya gabata ya auri Rosy da takardun bogi da sunan karya na Shaheen Alam dan Akram daga kauyen Kutuberchar a garin Shadhurpara da ke Bakshiganj Upazila, Gundumar Jamalpur.

Bayan Abu Baker, ya auri Rosy ya bukaci mahaifin Rosy ya biya sadaki kudin kasar da ya kai Naira 8,550, amma ya ki amincewa. Daga bisani ya karbi rancen kudin kasar da ya kai Naira dubu 342 da 175, sannan ya tsere da kudin bai biya ba.

Duk da auren mata 60 da Abu Baker ya yi yana da ’ya’ya bakwai ne kadai. Ya kasance yana yin auren ne kadai saboda kudi bayan an yi sai ya saki matar. Ya kasance yana amfani da takardun bogi a duk lokaci da ya bukaci yin auren kuma bai amfani da asalin adireshin gidansa na Islampur upazila.

Abu Baker, yana zaune a gidansa na asali ne da matarsa ta farko mai suna Sazeda Begum, da kishiyoyinta biyu da ’ya’yansu bakwai.

Babban jami’in ofishin ’yan sandan Islampur, Ansar Ali, mai binciken rahoton da aka gabatar ya tabbatar da cewa Abu Baker, ya auri mata 60 cikin shekara 25.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya