Da Dumi Dumi

An kama wanda ya sace jaririn wata daya a Ogun

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tabbatar kama wani mai suna Olakunle Agbaje mai shekara 39  akan zarginsa da sace jaririn wata daya a unguwar Mowe Karamar Hukumar Obafemi/Owode da ke jihar Ogun.

Wanda ake zargin ya sace jaririn ne a a gida mai lamba 32 yankin Adesan unguwar Mowe, sannan aka kama shi a unguwar bayan an sanarwa ofishin ‘yan sandan Mowe.

A wata sanarwa da kakakin hukumar ‘yan sandan Abimbola Oyeyemi, ya fitar na cewa, an sace jaririn ne lokacin da mahaifiyar jaririn mai suna Marufu Taiwo, ke barci a daki Olakunle ya shiga dakin ya dauke jaririn. Bayan dauke jaririn sai mahaifiyar jaririn ta farka daga barci daga bisani aka sanarwa jami’an ‘yan sandan yankin.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya