Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
An kama wani tsoho da jabun kudade a Kasuwar Maigatari

An kama wani tsoho da jabun kudade a Kasuwar Maigatari

Bazuwar kudin ganye a Kasuwar Maigatari da ke Jihar Jigawa ya tada hankalin ’yan kasuwa saboda yadda kudin ke zagayawa a kasuwar, lamarin da ya sa ’yan sanda suka dukufa wajen bincike domin gano ta inda kudaden suke shigowa kasuwar da nufin dakile su.

Sakamakon binciken ne ’yan sandan suka kama wani tsoho mai kimanin shekara 80 da ake kira Amadu Beti Dan Fulani da ke kauyan Dankargo a Karamar Hukumar Dingas a Jamhuriyar Nijar da jabun kudaden har Naira dubu 15.

Tsohon ya fada wa ’yan sanda cewa yana amfani ne da kudin wajen sayen lemon zaki yana tafiya da shi Jamhuriyar Nijar yana sayarwa.

Beti ya ce shi yana sayen kowace Naira dubu daya a kan Naira dari biyar shi kuma ya kawo  Najeriya ya batar da su a Kasuwar Maigatari maimakon a kasarsu Nijar kasancewar wanda ya ba shi kudin a Najeriya yake a kauyen Gumel, inda ya ce ana kai masa kudin ne har kauyensu ya saya ya biya.

Beti ya ce wani mutum ne mai suna Abu Kasuwa ke kai masa kudin ya saya, kuma wannan ne karo na biyu da ya kai masa jabun kudin ya saya. Ya ce ya kai masa Naira dubu 20 ya ba shi dubu 10, sannan ya kai masa dubu 15 ya ba shi dubu 7.

Beti ya ce ya san abin da ya aikata cuta ce, inda ya ce babu kyau a ce tsoho kamarsa yana wannan ha’inci. Ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata, inda ya nemi ’yan sanda su yi masa afuwa kada su kai shi gaban alkali, saboda ko yanzu ya san girmansa ya fadi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri ya tabbatar da labarin, inda ya ce ’yan sanda suna neman Abu Kasuwa da ke Karamar Hukumar Gumel ruwa a jallo.