✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wata mata da kwayoyi dubu da 600

Wata fasinjar jirgin sama da aka kama da kwayoyin turamol (tramadol) a dubu da 600 a akwatinta na tafiya a Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce…

Wata fasinjar jirgin sama da aka kama da kwayoyin turamol (tramadol) a dubu da 600 a akwatinta na tafiya a Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce don amfanin  kan ta,  domin a cewarta, ‘likita ne ya rubuta mata.

Kotun hukunta nmasu aikata miyagunb laifuka ta Abu Dhabi ta sameta da laifin shigowa kasar daga Masar da jakkarta cike da kwayoyin Turamol a filin jirgin saman kasar.

Jami’an kotun sun nuna hujjojin da suka tabbatar an kama matar a watannin da suka wuce, inda jami’an tsaro suka kama kwayoyin maganin.

Masu gabatar da kara sun bayyana yadda binciken jami’an hana fasakwauri suka bankado kwalayen magungunan da ke dauke da kwayoyin dubu da 600.

Matar da ta taso daga filin jirgin saman Alkahira, gwajin jininta ya nuna cewa tana shan kwayoyin maganin. Matar dai ta musa laifukan safarar kwaya da aka tuhumeta, in da ta doge kan cewa ita ta yi safar magungunan ne don amfganin kanta.

Da alkalin yanemi hujjar da ta hanata neman magani a Hadaddyar Daular Larabawa don nan ne take da zama, sai ta ce, ‘maganin cutarta kawai sai ta koma gida a kasarta ta haihuwa.’