✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ’yan kabilar Ibo 3 kan satar yara a Taraba

A farkon makon nan ne aka gurfanar da wata Ibo da ’yan uwanta biyu bisa zargin aikata laifin satar yara kananan yara a Jihar Taraba.…

A farkon makon nan ne aka gurfanar da wata Ibo da ’yan uwanta biyu bisa zargin aikata laifin satar yara kananan yara a Jihar Taraba.

Wadanda ake tuhumar masu suna Ruth Okoronkwo Anamechere da Heny Chidi Anamechere da kuma Emanuel Kelechi, an gurfanar da su ne a gaban Kotun Majistare da ke garin Jalingo. Wdanda ake tuhumar ’yan asalin wani kauye ne da ake kira Ummagu a Jihar Abiya da ke Kudu maso Gabas.

Mai gabatar da wadanda ake zargi a gaban kotun, Sufeton ’yan sanda Ankolmo Mela ya shaida wa kotun cewa an kama wadanda ake zargi ne a wurin da sojoji ke binciken ababen hawa tare da  wadansu yara biyu, Wisdom Felid ’yar shekara daya da rabi wadda ake zargin sun sace a garin Numan da ke Jihar Adamawa da kuma Ibrahim Aliyu mai shekara biyu da ake zargin sun sace a garin Iware da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola a Jihar Taraba.

Sufeto Ankolmo Mela ya bayyana wa kotun cewa wani mai suna Abdulmumini Adamu da ke zaune a rukunin gidaje na Inbestment a garin Jalingo wanda dansa ya bace ya zargi Ruth Okoronkwo daya daga cikin wadanda ake zargin ce ta sace dansa mai suna Salihu Abdulmumini a watan jiya.

Dan sandan ya kara da cewa wadanda ake zargin sun fadi cewa sun sace yaran ne da nufin kai su wajen wani mai suna Mista Onwa da ke Jihar Abiya su sayar masa da su. Ya ce laifin da ake zargin ya saba wa dokar satar mutane ta Jihar Taraba ta bana, wadda ke dauke da hukuncin kisa in hkotu ta tabbatar da laifin.

Matar da ’yan uwanta su biyu an kama su ne lokacin da suke kokarin tafiya da yaran zuwa Jihar Abia a cikin wata mota cike da hijabai na mata Musulmi.