✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ’yan Najeriya da suka kwace jirgin Birtaniya

Birtaniya ta kama wasu ’yan Najeriya 7 bisa zargin karkatar da wani jirgin ruwa mai dauke da danyen mai, Nave Andromeda, da ya tashi daga…

Birtaniya ta kama wasu yan Najeriya 7 bisa zargin karkatar da wani jirgin ruwa mai dauke da danyen mai, Nave Andromeda, da ya tashi daga Legas zuwa Southampton.

Ana zargin mutanen sun labe ne a cikin jirgin ruwan don samun mafaka ko tsere wa rikicin Najeriya, a ranar 5 ga watan Oktoba, 2020.

Wani dan sanda a Hampshire ya ce, “Ma’aikatan jirgin 22 na cikin koshin lafiya, jirgin kuma an ajiye shi a tashar jirgin ruwa ta Southampton”.

Ya ce mutanen da ake zargin sun tayar da rikici ne a daidai lokacin da jirgin ya tunkari tsibirin Wright, a ranar 25 ga watan Oktoba.

An ce sai da sojoji suka shiga cikin jirgin suka damke mutanen a tsibirin na Wright, a ranar Lahadi, kafin abin ya lafa.

Majiyar ta ce gabanin haka an jibge kwararrun matuka kananan jirgagen ruwa 16 na awa tara suna jiran ko ta kwana.

“Sauya akalar jirgin ta hanyar tsoratarwa ko tursasawa ya saba wa sashe na 9(1) da (3) na dokar jirgin sama da na ruwa da tsaro ta 1990”, inji jami’in.

Sakataren tsaro, Ben Wallace ya ce mutanen sun aikata laifin “Barazanar ga rayuwa”, kuma masu binciken na tattaunawa da ma’aikatan jirgin domin tabbatar da abin da ya faru.

“Akwai barazana ga rayuwar mutanen da ke cikin jirgin a lokacin da abin ya faru.

“Muna da labarin cewar mutanen da ake zargin sun yi barazanar yin wani abu da jirgin.

“Yunkurinsu na karkatar da jirgin kokarin sace shi ne da barazana ga muhalli da rayuwar mutanen da ke cikin jirgin wanda gwamnati ba za ta amince da shi ba”, inji Wallace.

BBC ta ruwaito cewar sojijin Birtaniya daga cikin helikwafta sun zura igiya suka sauka cikin jirgin a duhun dare.

Chris Parry, wanda tsohon sojan ruwa ne ya ce ba a dauki minti tara ba sojojin suka kwace jirgin.