Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An kama ’yar China da ta yi kutse a gidan hutawar Shugaban Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

An kama wata ’yar kasar China da ake zargi ta kutsa cikin jerin gidajen hutawa na Shugaban Amurka Donald Trump da ke Jihar Florida, inda kuma aka same ta dauke da wata na’urar kwamfuta a cikinta.

A cikin bayanan da lauyoyin da ke shigar da kara suka gabatar a gaban kotu, sun nuna cewa wannan matar mai suna Yujing Zhang ’yar asalin kasar China ta shiga rukunin gidaje na Mar-a-Lago ne da ke Palm Beach, inda gidajen hutu ne na Shugaba Trump, ta yi karyar cewa ita mamba ce a kulob din kuma tana son shiga wurin wanka na kulob din ne a lokacin da ta yi kutsen.

ADVERTISEMENT

Duk da cewa masu tsaron wurin ba su gano sunanta a jerin sunayen ’yan kulob din ba, sun bar ta ta shiga, inda daya daga cikin manajojin wurin ya bayyana cewa ya dauke ta a matsayin ’yar wata mace wacce ita ma mamba ce ta wurin.

Sai dai kuma bayan Yujing ta samu damar shiga cikin gidan, sai ta canja bayaninta, inda ta ce wai ta zo ne don ta halarci wani taro kan batun tatalin arziki a tsakanin Amurka da China.

ADVERTISEMENT

Daga baya sai aka gano cewa babu wani taron irin wannan da za a gabatar, sai aka tsare ta.